An gurfanar da wani matashi Benjamin Agbogu mai shekaru talatin da biyu a kotun majistire dake Igbosere a jihar Legas ana tuhumarsa da laifin satar zunzurutun kudi har Naira miliyan goma. Ana tuhumar matashin da laifuffuka biyu ne hadin baki da sata
Dan sanda mai gabatar da kara ASP Henry Obiazi, ya shaida wa kotu cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a watan Afirilun shekarar 2016 a garin Festac dake Legas, tare da wasu da har ake neman su ruwa a jallo.
Kuma yace wanda ake tuhumar yayi amfani da karfi akan Chukwu Chinedu, wanda yayi karar cewa an sace kudin daga wurinsa.
Laifin ya sabawa sashi na 287 (5) (a) da 411 na kudin laifukan jihar Legas na shekarara 2015, Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifin.
Alkalin mai suna Mr. B. A. Songua ya bada belin wanda ake tuhumar akan kudi Naira miliyan biyar da masu tsaya mishi mutum biyu.
Ya kuma tilas masu tsaya mishi su kasance manyan ma’aikata, kuma dole su nuna shaidar biyan haraji ga gwamnatin Legas domin tantance wajajen zaman su.
An daga saurarar karar zuwa 5 ga watan Disambar.