Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kutse Ya Kawo Cikas Ga Saukar Jiragen Sama


Wani sabon kutse ta yanar gizo ya durkusar da kwamfutocin filin saukar jiragen sama na kasar Ukraine da kamafanin tashar jirgin ‘kasa na kasar da kuma wasu kamfanoni yada labarai na kasar Rasha.

A bayyane yake kutsan yayi kama da irin wanda aka kai a watan Yuni, wanda ya karbe ikon kwamfutocin Asibitoci da ofisoshin gwamnati ya nemi a biya kudin fansa ko kuma ya goge duk wasu bayanai da ke cikin na’urorin.

Wani kamfani dake bayar da tsaro a yanar gizo, ya fada a wata sanarwa da ya fitar cewa wata manhajar kutse da ake kira da suna BadRabbit ta yi kokarin karbe ikon kwamfutocin manyan bankunan kasar Rasha, amma bata samu nasara ba. don babu bankin da ya bayar da rahotan an yi masa kutse.

Kamfanin Kaspersky na kasar Rasha ya ce yana sane da cewa sama da kamfanoni 200 a kasashen da suka hada da Rasha da Ukraine da Turkiyya da kuma Jamus ake kai musu hari.

Kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa, Interfax, tun ranar Talata ya mika kukansa kan wannan batu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:10 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG