Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, dake Kasar Ingila, ta nada Claude Puel a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasanta, wanda ya maye gurbin tsohon mai horar da ‘yan wasan watau Shakespeare, wanda kungiyar ta sallama a satin da ya gabata, sakamakon rashin tabuka wani abun kirki tun da ya karbi ragamar kungiyar.
Claude Puel mai shekaru 56, haifaffen n kasar Faransa ne kuma ya kasance tsohon dan wasan tsakiya mai tsaron baya na kungiyar kwallon kafa ta Monaco daga shekara 1979 zuwa 1996 ya kuma samu buga wasannin 488, a lokacin kuma kwallaye hudu kacal ya jefa a raga.
Claude, ya zamo mai horar da ‘yan wasa a 1999 inda ya jagoranci kungiyoyi da dama, irin su Kungiyar Monaco, Lille, Lyon da Nice, duka a kasar Faransa, daga bisani ya tsallaka zuwa kungiyar Southampton na kasar Ingila, 2016, inda ta sallameshi a shekara ta 2017 bisa wasu dalilai.
Mai horar da ‘yan wasan ya rattaba hanu a kungiyar ta Leicester city na tsawon shekaru uku.
Mataimakin kungiyar ta Leicester City,Mr Aiyawatt Srivaddhanaprabha, yace yana da tabbacin cewa Claude na da kwarewa sosai, kuma zai farfado da kungiyar daga cikin halin da take ciki.
Facebook Forum