Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hafiz Ibrahim: Gudun Mawar Matasa 'Yan Najeriya A Duniya Bata Misaltuwa


Hafiz Ibrahim Ahmed
Hafiz Ibrahim Ahmed

Hafiz Ibrahim Ahmed, dan asalin jihar Katsina ne, wanda ya samu nasarar kammala karatun shi na matakin firamari har zuwa sakandire duk a cikin birnin Katsina. Wanda daga bisani ya samu damar zuwa jami'ar Bayaro Kano inda yayi karatu a matakin digirin farko a fannin Chemistry.

Hazakar Hafiz da kwazo yasa, ya samu gurbin karatu a karkashin tallafin hukumar rarrar mai ta kasa PTDF, Inda ya tafi kasar Burtaniya ya kuma samu damar kammala karatu a matakin digiri na biyu, "Master in Analytical Chemistry" a Jami'ar Huddersfield duk a kasar ta burtaniya.

Hafiz, bai tsaya nan ba ya sake neman gurbin karatu a matakin digirin digirgir, inda yake zurfafa bincike, da zummar gano hanyoyi da za'a magance kananan kwayoyin cututtuka dake hallaka jama'a.

Babban burin Hafiz, shine ya bada tashi gudunmawa wajen kawo karshen cututtuka a kasashen Afrika, musamman gida Najeriya, bayan kammala karatun shi. Ya zuwa yanzu yana ci gaba da fadada bincike wurin kiwon lafiya, don ceto da rayuka.

Hafiz, yana mai kara jawo hankalin matasa da cewa, su tashi su nemi ilimi, ka da su zama ci ma zaune, kar su bari zuciyar su ta mutu, saboda tuni anyi ma matasan Arewa nisa a bangare na ilimin zamani. Akwai tallafi daban-daban na karatun masu yawa, wanda matasan mu zasu iya nema don karo ilimi a kasashen da suka cigaba a fadin duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG