Wani Matashi Mai Shekaru 25 Ya Yiwa Wata Nakasasshiya Fyade

An kama wani Matashi mai shekaru ashirin da biyar (25), mai suna Sunday Aremu, da laifin sace wata nakasasshiya da kuma yi mata fyade.

An gurfanar da Aremu, a kotun Magistrate din dake Ebute Meta , a birni Lagos .

Shida Aremu, ana tuhumarsa ne da laifin hada baki tsare mutun ba a son ransa ba dakuma yin fyade, laifin da ya amsa batare da gaedama ba.

Mai gabatar da kara Sgt. Kehinde Omisakin, ya fadawa kotu cewa Aremu, ya aikata laifin ne a ranar 13, ga watan Afrilu da misalign karfe daya na rana a garejin mota dake Ojota, a wajen garin Lagos, inda kuma ya ajiye yarinya har na tsawon kwanaki gima sha hudu.

Laifin ya sabawa dokar jihar Lagos , sashe na 137 na 144 da kuma na 411 na shekarar 2015, mai shara’a A.T Elias, ya dage karar zuwa 17, ga wannan wata da muke ciki.