A wasan da aka buga na gasar cin kofin Turai Europa League na shekarar 2016/17 a jiya kungiyar kwallon kafa ta Manchester united ta doke takwararta ta Celta Vigo, ta kasar Spain da ci daya mai ban haushi a gidan Celta Vigo.
Manchester, ta samu nasarar kwallon ne ta kafar dan wasanta Marcus Rashford, a cikin mintuna na 67 da fara wasan.
Rabon Manchester United, ta doke wata kungiya a kasar Spain, bangaren gasar Turai a matakin kihuwa daya (Nock Out) shekaru tara kenan
tun a shekarar da ta samu nasara akan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, a shekara 2008 a gasar zakarun nahiyar Turai wanda a wannan shekarar Manchester ta lashe kofin akan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, a bugun daga kai sai mai tsaron gida (Penalty)
A ranar Alhamis 11/5/2017 za'a fafata a zagaye na biyu a gasar ta Europa league
Inda Lyon zata kara da Ajax wanda ta lallasa ta 4-1
Manchester United, zata karbi bakuncin Celta Vigo a kasar Ingila.