Wani Matashi Ya Yiwa Mai Shekaru 65 Fyade

Bacci ya kwashe wani matashi mai shekaru ashirin bayan ya akatawa wata dattijuwa mai shekaru sittin da biyar fyade a dakin ta a garin Nkayi a kasar Zimbabwe.

Matar ta shaidawa mai shara’a cewar bayan ya gama amfani da ita, matashi ya sanar da ita cewa yanzy ta zama mallakin sa, a cewarta, daga nan ne bacci ya dauke shi a cikin bargon ta.

Ta ci gaba da cewa, matashin wanda ya kasance makwabcin ta ya shake ta ne tare da tambayarta ko tana shan maganin kariya daga cuta kamar kanjamau watau HIV.

Ta sanarwa da kotu cewa tayi kokarin kwatar kanta amman batayi nasara ba har ya samu damar cin karfin ta.

Tace bayan yayi bacci a kan gadonata, sai ta sulale da jikar ta yar shekara biyu ta gudu gidan makwabta daga bisani, ya tashi daga baccin ya gudu.Ta kara da cewa tana jin tsoron kwana a gidan kokuma hada ido dashi saboda abinda yayi mata.

A cewar jaridar chronicle, wanda ake kara bai amsa laifin shi ba lokacin da ya gurfana a gaban alkali Trynose Utahwashe wanda ya jefa shi a gidan kaso har zuwa biyu ga watan Nuwamba, lokacin da za a ci gaba da saurarr karar.

Matsahin yace babu yadda za ayi yayi wa matar da tayi sa’a da mahaifiyar shi fyade.

Dan sandan mai gabatar da kara yace lallai wanda ake tuhumar yayi wa matar fyade ne lokacin da take bacci a gidanta.