Shahararen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Manchester United, na kasar Ingila mai suna Zlatan Ibrahimovic, yace yana daf da dawowa filin wasa, da karfin gwiwarsa. bayan da ya dauki tsawon lokaci yana jinya.
Dan wasan wanda ya samu rauni a gwiwarsa tun kafin kammala wasannin 2016/17, dan wasan mai shekaru 36, da haihuwa dan kasar Sweden, yace zai dawo filin taka leda da da nufin karasa aikin da ya fara.
Zlatan kwararren dan wasan gaba ne wanda yazo kungiyar Manchester United a 2016, a matsayin kyauta ya kuma taimaka wa kungiyar ta Manchester United, wajen lashe kofuna har guda uku, a zamansa da yayi na shekara daya kachal wanda suka hada da kofin Community Shield, Europe league, da kuma English Football League, duka a 2016/17.
Zlatan Ibrahimovic yace sauran aikin da ya rage masa a kasar Ingila shine lashe kofin Firimiya lig na bana 2017/18, ya kara tsawaita zamansa a Manchester United na shekara daya bayan da kwangilarsa ya kare a 2017.
Dan wasan ya shaida wa Sky Sports cewar yana sa ran dawowa fagen taka leda a watan Disamba 2017.
Facebook Forum