A Pakistan Wani Dalibi ya Mutu a Yayinda Yayi Yunkurin Hana Dan Kunar Bakin Wake Isa Makarantarsu

Hoton Aitzaz Hassan wanda ya hana dan kunar bakin wake kaiwa ga makarantarsu.

Saboda haka 'yar gwagwarmayar nan Malala tace zata bada gudumawar rabin milyan daya a kudin Pakistan ga iyayen dalibin.
‘Yar gwagwarmayar nan budurwa daga Pakistan, Malala Yousufzai, ta fada jiya jumma’a cewa zata bada gudumawar rabin milyan na kudin Pakistan, kimanin dala dubu biyar, ga iyayen wani matashi dan shekaru 15 da haifuwa wanda ya rasa ransa a kokarin da yayi na hana wani dan harin kunar bakin wake kai hari kan makarantar da yake zuwa.

Haka kuma Malala tayi kira ga gwamnatin kasar Pakistan ta karrama mamacin Aitzaz Hassan, da babbar lambar girmamawa da kasar take baiwa farar hula da suka yi fice ko nuna bajinta. An kashe matashin ne ranar litinin a gundumar Hangu dake cikin lardin Khyber pakhtunkhwa, dake can da nesa cikin kasar.

Ita malala dai ta rayu bayanda ‘yan bindiga daga kungiyar Taliban suka kai mata hari tana ‘yar shekaru 12, a yankin kwazazzabun Swat a shekara ta 2012. Malala tayi fice a duk fadin duniya, saboda adawarta kan mayakan sakai, da kuma jajircewa kan hakkin diya mata su nemi ilmi.

‘Yansanda a yankin suka ce Aitzaz wanda yake makarantar sakandare, yaga maharin lokcinda ya fito daga cikin wata motar safa ya doshi makarantarsu. Mutumin yana saye da uniform din makarantar, amma akwai alamun yana da wata muguwar anniya. A lokacin ne Aitzaz yayi kokarin hana shi isa makarantar, lamarin da ya tilastawa maharin tada nakiyoyi da yayi guru da su.

'Yayan Aitzaz, Mujtaba, ya gayawa tashar Rediyon Deewa ta Muriyar Amurka cewa, uwar matashin tayi kukan rashin danta, amma matakin inji uwarsa ya hana wasu uwaye su 500 kuka. Dalibai dari biyar ne suke makarantar.