Jiya Juma'a da safe, kudurin da aka gabatar na dage yin shari'a da ake yiwa Uhuru Kenyatta shugaban Kenya da mataimakinsa William Ruto da tsawon watani goma sha biyu ya gaza samu kuri'ar da ake bukata da kuri'a biyu kacal.
Bakwai daga cikin wakilan kwamitin goma sha biyar ne suka jefa kuri'ar amincewa wannan mataki, yayinda takwas kuma suka jefa kuri'ar rashin amincewa.
Wannan kuduri da kasashen Afrika suka gabatar yana bukatar akalla kuri'u tara, ba tare da hawan kujeran naki daga wakilan kwamitin na dindindin su biyar ba.
Ana caji Mr. Kenyatta da mataimakinsa da aikata wa bani Adamu laifuffuka bisa zargin cewa sun shirya tarzomar bayan zabe a shekara ta budu biyu da bakwai da kuma shekara ta dubu biyu da takwas data kashe fiye da mutane dubu daya da dari daya. Dukkan shugabani biyu sun musunta zarge zargen da ake yi musu.
Kasashen da suka gabatar da kudurin dage shariar, Rwanda da Togo da kuma Morocco sun jefa kuri'ar amincewa tare da Rasha da Azerbaijan da kuma Pakistan. Amirka da Ingila da Faransa suna daga cikin kasashen da suka kauracewa jefa kuri'a akan kudurin.