Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Miliyan 230 Basu Taba Samun Rejistar Haihuwa Ba


UNICEF
UNICEF

Yara miliyan 230 ‘yan kasa da shekara biyar a duk fadin duniya ne basu da rijistar haihuwa, wanda ya ke nuna ba lallai su sami ilimi, kiwon lafiya, ko cikakkar kulawa daga gwamnati ba, inji hukumar yara ta majalisar dinkin duniya.

Yara miliyan 230 ‘yan kasa da shekara biyar a duk fadin duniya ne basu da rijistar haihuwa, wanda ya ke nuna ba lallai su sami ilimi, kiwon lafiya, ko cikakkar kulawa daga gwamnati ba, inji hukumar yara ta majalisar dinkin duniya.

Ruhuton da hukumar dake kula da yara ta majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta fitar a ranar laraba lokacin bikin cikar ta shekara 67 da kahuwa, ya nuna cewa yaro daya daga cikin uku ‘yan kasa da shekara biyar bashi da rijistar.

A bara, hukumar tace kashi 60 daga cikin dari na dukan yaran da aka Haifa sun sami rijista lokacin haihuwa sai dai inda rejistar tafi karanci shine a yankin Asia da kuma sashen Afrika dake kudu da hamada.

Mataimakin direkta na UNICEF Geeta Rao Gupta yace yiwa yara rijista ba shaida kawai bace ta cewar an san da zaman yaron, amma “Tabbaci ne na cewa ba za’a manta da wadannan yaran ba, ba kuma za’a danne masu hakakkinsu ko a barsu baya a sha’anin cigaban kasarsu ba.

“Rijistar haihuwa – da katin shaidar haihuwa – na da mahimmanci sosai wajen budewa yaro hanyar ci gaba.,” inji Rao Gupta. “Idan al’umma bata kirga su ba, bata kula da kasancewarsu ba, yin watsi dasu da kuma cin zarafin su ba zai yi wuya ba. A karshe duka, za’a dakile baiwarsu.

UNICEF tace rashin kirga yara, ba yana hana masu damar karatu, kiwon lafiya da walwala bane kadai, amma yana shafar ci gaban al’umma da kasa baki daya. Ta bayyana dalilai dake kawo cikas ga yin rijistar haihuwar yara, tun daga iyaye da basu da cikakkiyar fahimtar mahimmancin ta zuwa dalilai na al’adu da tsoron sakamakon da zai biyo bayan sanarwar haihuwar yaro wanda suka hada da rashin asirta bayanan mutane kamar launin fata, addini ko haihuwa ba cikin aure ba.

Rahoton yace yaran da ke zama a kauyuka, ‘ya’yan marasa galihu, wadanda iyayen su basu da ilimi sun fi fuskantar rashin rijista.

UNICEF tayi kira da a bullo da shirye shirye wadanda zasu yaki dalilan dake kawo rashin yin rijistar yara, wanda suka hada da tsawala kudin yin rijista da rashin fahimtar ka’idodi da matakan yin rijistar.

Kasashe 10 da suka fi karancin rijistar haihuwa in ji UNICEF, sune Somaliya kashi Uku cikin dari, Liberiya kashi hudu cikin dari, Habasha kashi bakwai cikin dari, Zambiya kashi sha hudu cikin dari, Chadi da Tanzaniya kaso sha shida cikin dari, Yemen kaso sha bakwai cikin dari, Ginea bisau kaso 24 cikin dari, Pakistan kashi 27 cikin dari da Kongo kashi 28 cikin dari.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG