WASHINGTON, DC —
Sakataren harkokin tsaron Amurka Chuck Hagel yayi kashedi ga mahukuntan Pakistan cewa muddin basu kawo karshen zanga zangar da take dakatar da jigilar kayayyakin NATO daga Afghanistan da suke ratsawa ta cikin kasar, hakan yana iya illa ga irin tallafi da kasar take samu daga Washington.
Hagel yayi wannan gargadin ne a ziyarar da ya kai Pakistan, wacce itace ta farko da wani babban jami'in ma'ikatar tsaron Amurka zai kai kasar a kusan shekaru hudu. Ziyarar d a kuma zanga zanagar duka suna zuwa ne a dai dai lokacin d a Amurka take rage dakarunta a Afghanistan makwabciyar Pakistan din.
Sakatare Hagel ya gana da PM Pakistan Nawaz Shariff da kuma sabon babban hafsan hafsoshin kasar, Janar Raheel Sharif.