Wasu abubuwa daga cikin littafin akan shugabancin Trump, da wani dan jarida da aka ce ya taimaka wajen kawas da Richard Nixon daga kujerar mulki, ya bayyana gwamnatin Trump a matsayin wadda ke fuskantar juyin mulki da rashin kwanciyar hankali a cikin watanni 19 da kafa gwamnatinsa.
Littafin mai suna Fear: Trump in the White House, mai shafi 448 wanda Bob Woodward ke shirin fiddawa ranar 11 ga watan nan na Satumba, ya bayyana yadda hadimai ke kwashe takardu daga teburin Trump da kuma yin wasu abubuwa da suka kaucewa kudurorin shugaban. Littafin ya kuma bayyana Trump a matsayin “kidahumi” akan lamuran dake faruwa a duniya kuma fadarsa ba ta aiki yadda ya kamata, sannan kuma cike take da rigingimu kala-kala.
Kodayake ‘yan jarida da tsofaffin ma’aikatan fadar White House sun taba bayyana kwamacalar da ta dabaidaye fadar a baya.