Isra’ila ta kai wani kan wani ginin makaranta a Gaza da sanyin safiyar Assabar, inda ta kashe mutane akalla 80 tare da raunata wasu kusan 50, a cewar hukumomin lafiya na Falasdinu.
Wannan na daya daga cikin hare-haren mafi muni na yakin Isra'ila da Hamas na tsawon watanni 10. Wani ganau ya ce lamarin ya afku ne a lokacin sallah a wani masallaci da ke cikin ginin.
Wannan dai shi ne na baya-bayan nan na abin da ofishin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana da "Hare-hare kan makarantu a wayance" da Isra'ila ta kai, tare da a kalla hare-hare 21, tun daga ranar 4 ga watan Yuli, inda kuma suka hallaka daruruwan mutane, ciki har da mata da kananan yara.
"Ga mutane da yawa, makarantu sune mafita na karshe da jama’a ke samun mafaka," in ji MDD bayan harin na ranar Assabar.
Rundunar sojin Isra'ila ta amince tare da bayyana kai hari kan makarantar Tabeen da ke tsakiyar birnin Gaza, inda ta ce ta kai hari kan cibiyar ayukan mayakan Hamas a wani masallaci da ke harabarta tare da kashe mayakan Hamas 19 da mayakan Jihadin Islama.
To sai dai Izzat al-Rishq, wani babban jami'in Hamas, ya musanta cewa akwai mayaka a cikin makarantar.
Rundunar sojin ta Isra'ila ta kuma musanta adadin mutanen da aka ce an kashe, tana mai cewa makaman da aka yi amfani da su "ba za su iya haddasa yawan barnar da gwamnatin Hamas ta ba da sanarwa ba.
Ta ce matakan da ta dauka na takaita lahani ga fararen hula sun hada da yin amfani da kananan makamai, sa ido ta sama da kuma tattara bayanan sirri.
Fadel Naeem, darektan asibitin al-Ahli da ke birnin Gaza, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, sun karbi gawarwaki 70 tare da sassan jikin akalla wasu 10. Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce wasu mutane 47 sun jikkata.
A baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa ranar 6 ga watan Yuli, makarantu 477 daga cikin 564 da ke Gaza an kai musu hari kai tsaye ko kuma an lalata su a yakin, inda ta kara da cewa Isra'ila na da hakki a karkashin dokokin kasa-da-kasa na samar da mafaka ga 'yan gudun hijirar.