Rahotanni daga rundunar ‘yan sandan jahar Lagos na cewa mutanen sun rasa rayukansu ne sakamakon rushewar ginin, wanda kuma ya kamata a rushe ginin tun a shekara ta 2014, amma kuma aka bar mutanen ke zaune cikin sa ba tare da an tashe su ba.
A cewar kwamishinan ‘yan sandan jahar Lagos, Fatai Owoseni, tuni ya bayar da umarnin a rushe wannan gini tare da sauyawa mutanen dake zaune a ginin matsugunni.
Rushewar gine gine a Najeriya ba wani sabon abu bane, domin a baya-bayannan ma wata Majami’a ta rushe a yankin Kudi maso Kudancin Najeriya, inda ya kashe mutanen da dama, a jahar Lagos dai an sha samun rahotannin rugujewar gine-gine al’amarin da yake haifar da mutuwar bil Adama.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Your browser doesn’t support HTML5