Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gudun Hijira Sun Sami Tallafin Kayayyakin Kirsimeti a Adamawa


Mata ‘yan gudun hijira Musulmai da Kirista dubu biyu da dari biyar sun anfana da tallafin abinci albarkacin bukin Kirismeti a Yola fadar jahar Adamawa.

Da yake rabon tallafin abincin limamin darikar Katolika Bishop Dakta Stephen Dami Mamza, yace sun yi la’akari da ‘yan gudun hijirar da basa zaune a sansanoni, wadanda ba ko wanne lokaci suke amfana daga kayayyakin tallafin da ake baiwa ‘yan gudun hijira ba, musamman wadanda ke kauyuka kuma basu da sukunin yin Kirsimeti.

Da ta ke jawabin godiya ga taimakon da suka samu daga Majami’a, mai magana da yawun ‘yan gudun hijiran Malama Lami Danlami, ta yi kakkausar suka ga hukumomin kai dokin gaggawa da kungiyoyin da ke tallawa ‘yan gudun hijira da nuna son zuciya da cusa siyasa a lamuran da suka shafi ‘yan gudun hijira. Zargin da Bishop Stephen Dami Mamza ya nuna takaicinsa ya kira da kamata ya yi su sake daidaita ayyukansu.

Wasu mata ‘yan gudun hijira da muryar Amurka ta yi hira da su sun ce sun zubawa Allah ido suna jiran sarautarsa, saboda rashin abin da zasu yi bukin Kirismeti da shi kafin tallafin abincin ya shiga hanunsu.

Kokarin da wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, ya yi ta hanyar sakon kar-ta-kwana da wayar selula don jin ta bakin shugabannin hukumomin kai dokin gaggawa ta tarayya da jaha kan wanna zargin a daidai lokacin hada wannan rahoton ya cutura.

Domin karin bayani saurari sauran rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG