Wani Dan Najeriya Yace Ya Gano Maganin COVID-19

Madagascar Ta Aika Wa Tallafin Maganin Coronavirus

Wani dan Najeriya ya yi yi kirarin cewa ya harhada maganin gargajiya da tsirai da ya hakikanta zai yi maganin cutar Korona sai dai jami'an lafiya sun ce babu tabbacin haka

Masanin kimiyar halittun ya yi ikirarin yana da maganin gargajiya na COVID-19 da ya fi maganin kasar dake tashe na kasar Madagaska da likitocin basu tabbatar da tasirin shi ba inganci –Sai dai hukumomin lafiya sun yi gargadi da cewa, a yi taka tsantsan, kuma tilas ne a gwada magungunan na gargajiya kafin amfani da su in ba haka ba illarsu zata yi muni fiye da amfanin su.

Masanin kimiyyar halittun Na Najeriya, Innocent Ogbonna ya yi ikirarin cewa ya harhada maganin gargajiyan da tsirrai.

Kamar yadda ya faru a Madagaska, tawagar da suka yi bincike da Ogbonna sun yi ikirarin cewa, magani gargajiyar su yana taimakawa marasa lafiyar COVID-19 su samu lafiya daga kwayar cutar.

Amma hukumomin kiwon lafiya sun yi gargadin cewa ana bukatar gwaji kafin ayi amfani da magungunan gargajiyar wajen jinyar COVID-19.

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, Dr. Nathan Shehu, likitane mai kula da cuttuka masu yaduwa a asibitin koyarwa na jam’iyar Jos ya ce “Gaskiya akwai magungunan gargajiya kuma za su iya yin maganin COVID. Amma yana da muhimmaci kafin a fito da su domin irin wannan dalili, dole ayi gwaje gwaje don tabbatar da inganci ko suna aiki ko ba sa yi. Saboda kana batun rayukan mutane ne."