Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Najeriya Sun Amince Daliban Sakandare Su Rubuta Jarrabawar Karshe


Yemi Osibanjo Ya Ziyarci 'yan Makaranta
Yemi Osibanjo Ya Ziyarci 'yan Makaranta

Nan da makonni biyu masu zuwa ne ake sa ran dalibai a kasashen nahiyar Afrika ta Yamma zasu fara rubuta jarabawar kammala sakandare.

Hakance ta sanya hukumomin ilimi a Najeriya suka amince daliban dake ajin karshe na sakandare su koma makaranta a jiya Talata, amma a jihohin Kano da Kaduna za a bude makarantun ne a ranar Litinin ta makon gobe.

An kwashe shekaru da dama dalibai na rubuta wannan jarabawa ta kammala sakandare a Afrika ta Yamma a watannin Mayu da Yuni na kowace shekara, amma annobar corona ta sanya a bana sai a watan Agusta ne za a fara jarabawar.

Tuni dai ma’aikatar ilimi ta Najeriya bisa shawara da kwamitin yaki da cutar coronavirus na kasa suka amince a bude makarantun sakandaren Najeriya a jiya Talata, amma ga daliban dake kammala karantu kawai.

Gabanin wannan ci gaba, a baya hukumomin Najeriya sun tsame kasar daga jerin kasashen Afrika ta Yamma da daliban su zasu rubuta wannan jarabawa a bana saboda wannan larura ta Corona.

Sai dai wannan mataki na gwamnatin Najeriya ya sha caccaka da suka daga wasu daga cikin masana harkokin ilimi na kasar dama mamallaka makarantu masu zaman kansu.

Farfesa Usman Da’u Aliyu na Jami’ar Bayero Kano na cikin wadanda suka bayyana rashin gamsuwa da hukuncin gwamnatin Najeriya a wancan lokaci.

Ta yiwu hakance ta sanya, Comrade Yahya Shu’aibu Ungogo wani mai sharhi kan lamura ke cewa, akwai bukatar hukumomi su sake garanbawul ga tsarin ilimin Najeriya.

Har yanzu iyaye da dalibai na dakon sanarwar hukumomin Najeriya game da lokacin da za a bude makarantun Pramare, Jami’o’I da sauran manyan makarantun ilimi mai zurfi.

Daga Kano ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG