Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Duba Yiwuwar Hada Hannu Da Kamfanoni Masu Zaman Kansu Don Gwajin COVID-19


Hukumomin Najeriya na duba yiwuwar kulla kawance tsakanin gwamnatocin jiha da kamfanoni masu zaman kansu don kara yawan gwaje-gwaje da neman wadanda suka kamu da cutar coronavirus

Hakan na zuwa ne yayin da aka shirin maido da zirga zirgar jiragen sama na kasa da kasa da kai fara aiki a wannan watan na Agusta, in ji shugaban hukumar NCDC ta Najeriya mai sa ido kan cututtuka masu yaduwa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito yana cewa.

Ranar 29 ga watan Agusta za a bude tashar jiragen sama ta kasa da kasa.

Tun daga ranar 23 ga watan Maris aka rufe tashar sai dai jiragen da ke zuwa ketare don taimakawa wajen yaki da annobar COVID-19 ne suka yi aiki a kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afrika.

Gwamnatocin jihohi ke da alhakin yin gwaji da nemo wadanda suka kamu da cutar amma shigowar matafiya da yawa zai kara nauyi akan hukumomin da dama aikin ya yi musu yawa a Najeriya, kasar da yanzu ta ke da mutum 50,488 da suka kamu da cutar da kuma mace-mace 985.

Lagos, jihar da cutar ta fi kamari a Najeriya, na da masu nemo wadanda suka kamu da cutar 200 a jihar da ke da al’umma miliyan 25, wato zasu nemo kasa da mutum 1 cikin 100,000 kenan, idan aka kwatanta da nemo kusan mutum 14 cikin 100,000 a kasar Turkiyya a misali.

Shugaban hukumar ta NCDC Chikwe Ihekweazu ya ce an tattauna da kamfanoni masu zaman kansu akan yiwuwar kawancen don gwaji da kuma nemo wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG