Wani Da Ba Direban Jirgi Ba, Ya Dauki Jirgi Kuma Ya Fadi Da Shi

Jirgin Amurka

Wani ma’aikacin kamfanin jirgin sama a birnin Seattle na jihar Washington ya saci jirgi ya tashi da shi, kana ya yi wasan nuna bajinta kafin jirgin ya yi hatsari a tsibiri Ketron dake kudancin Puget, mai cike da dimbin jama’a da yammacin jiya Juma’a.

Babban jami’in 'yan sandan karamar hukumar Pierce ya fada a wani sakonsa na Twitter cewa dan shekaru 29 da haifuwar kuma ma’aikacin kamfanin jirgin saman, ya dauki jirgin ne mai tagwayen inji daga filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Takoma dake birnin Seattle. Babban dan sanda ya kwatanta wannan lamari da kisar kai.

Masu kula da zirga zirga jiragen sama sun ce sun ji ana kirarsa da suna Rich, ana ce masa ya sauka da jirgin.

Conostance von Muehlen shine babban jami’in aikin kamfanin jiragen sama na Horizon Air, ya fada a sakonsa na Twitter yana mai cewar muna mika ta’aziyarmu ga iyalan mutane dake cikin jirgin da ma ma’aikatarmu na Horizon Air da Alaska Air.

Sai dasi kamfanin na Horizon Air bai bayyana sunan mutumin da ya mutu a cikin hatsarin jirgin na yammacin jiyan ba.