Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 'Yan Majalisa A Jihar Ohio Ya Dauke Hankali A Amurka


Majalisar Amurka
Majalisar Amurka

Zaben na musamman na 'yan majalisar wakilan Amurka da aka gudanar a jihar Ohio, ya dauke hankali a yau Laraba, yayin da 'yan Republican da Democrat suke lura da yanda sakamakon zai kaya, wanda zai tabbatar da yanda zaben rabin wa’adi na fadin kasar zai tafi a cikin watan Nuwamba mai zuwa.

Ratar tsakanin dan Republican Troy Balderson da ya wakilici jihar a majalisar dattawa sau biyu da kuma dan Democrat Danny O’Connor, jami’in adana bayanai a karamar hukumar Franklin bata da yawan da za a iya ayyana mai nasara.

Ana nan ana ci gaba da kirga kuru’u, yayin da 'yan takarar ke ci gaba da nuna sun yi nasara duk da rashin samun ratar da zata raba gardama.

Dan takarar na Democrat Danny O’Connor, ya fadawa taron magoya bayansa cewa, muna cikin wata gasa mai karfi kuma kune kuka sanya haka. Ina nufin ku talakawa da kuke neman kakkyawar makomar ga kasar mu. Ina matukar godiya da wannan goyon baya da kuka kyautata mana zato a wannan takarar, da abokan karawarmu suka ce bamu zamu kai labari ba. Kun nuna musu ba haka lamarin yake ba.

Shugaba Trump ya ayyana nasara ga Balderson dan takarar Republican a wani sakonsa na Twitter, domin karawa kempensa da ya yi a kurarren lokaci tasiri, a gundumar da ya lashe da maki 11 a baya.

Bladerson ya godewa Trump da mara masa baya, ya kuma karfafawa kansa gwiwar doke abokin takararsa O’Connor.

Yace jikin Daniel O’Connor ya yi tsami a wannan takara, kuma ina zuba ido in fafata da shi a kakar zaben bana.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG