Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Kirkiro Rundunar Sojin Sararin Samaniya


Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence yayinda yake sanar da shirin kirkiro rundunar sojin sararin samaniya nan da zuwa shekarar 2020
Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence yayinda yake sanar da shirin kirkiro rundunar sojin sararin samaniya nan da zuwa shekarar 2020

Nan da zuwa shekarar 2020 Amurka za ta kirkiro rundunar sojin sararin samaniya a cewar Mike Pence, mataimakin shugaban Amurka wai domin kawar da barazanar da China da Rasha ke yiwa tsaron Amurka abun da wani dan majalisar dattawan kasar na jam'iyyar Democrat ya kira shirme

Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, ya ce ma’aikatar tsaron Amurka da ake kira Pentagon, ta fara daukan wasu sabbin matakai na kirkiro da rundunar soji ta sararin samaniya nan da shekarar 2020, da nufin zama cikin shiri domin barazanar da ka iya tasowa a wannan sabon filin-daga.

Yayin da yake jawabi a ma’aikatar tsaron ta Pentagon a jiya Alhamis, Pence ya ce “lokaci ya yi da za a rubuta wani sabon babi a tarihin darakunmu, domin su zauna cikin shirin zuwa fagen-daga na gaba - yana mai cewa lokaci ya yi da Amurka za ta kafa dakarun duniyar samaniya.

Shugaba Donald Trump ya sha kiran da a kafa rundunar ta sama -jannati a matsayin wani sabo reshen soji, domin Amurka ta samu damar mamaye sararin na samaniya.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a shafinsa, Sanata Brian Schatz, dan jam’iyyar Democrat mai wakiltar jihar Hawaii ya kwatanta wannan batun na kirkiro da dakarun a matsayin “shirme.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG