Kasar Japan ta ce Koriya ta arewa na cigaba da zama bababar barazana ga tsaron kasarta, duk da alamar daukar salon diplomasiyya da gwamnatin kasar ta nuna a idon duniya.
Abinda aka gano kenan a wani bincike da aka yi akan manufofin tsaron kasa na shekara shekara da kasar Japan ta wallafa yau Talata.
Rundunar sojan kasar ta lura cewa koriya ta arewa ta yi wasu gwaje-gwajen nukiliya guda 3, ta kuma harba makamai masu linzami sama da 40 tun daga shekara ta 2016, kuma wasu daga cikin su sun bi ta saman Japan. Gwamnatin ta Japan ta ce tana shirin sayen na’urorin garkuwa dake hango makamai masu linzame guda 2 kirar Amurka don kare kasar ta daga yiwuwar harin makami mai linzame daga koriya ta arewa.
Rahoton ya yaba sabon matakin diplomasiyya da koriya ta arewa ta runguma da abokiyar gabarta koriya ta kudu da kuma Amurka, wanda ya kai ga taron kolin tarihi da aka yi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban koriya ta arewa Kim Jong Un a Singapore ranar 12 ga watan Yuni, a lokacin da duka shugabannin suka rattaba hannu a wata takarda da ta kunshi alkawarin da koriya ta arewa ta yi na dakatarda shirin makaman ta na nukiliya.