Gwamnatin Afghanistan ta ce Rasha ta dage har illa masha'Allahu taron sulhu da aka yi niyyar yi sati mai zuwa gameda kasar ta Afghanistan.
A cikin sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban Afghanistan a ranar Littini, ta bayyana cewa Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan sun cimma matsaya cewa a dage wannan taron har zuwa wani lokaci nan gaba.
A cikin sanarwar, Ghani ya bayyana cewa wannan taron kamata ya yi ya zamo kasar ta Afghanistasn ce ta shirya shi kuma take shugabantansa.
Shima Lavrov ya ce ba shakka sun amince cewa wannan taron ya zamo karkashin kulawar Afghanistan kuma Rasha a shirye take ta ba ta dukkan goyon bayan da take bukata.
Sai dai a wuri daya kuma jami’an kasar Afghanistan sun ce wani jirgin sama daga makwabciyar kasar wato Tajikistan ya kai hari a bakin iyakar kasar da ya kashe wasu dillalan miyagun kwayoyi harsu 6, wannan ko ya biyo bayan bata kashin da akayi ne a bakin iyakan wanda ya yi musabbabin mutuwar jami’an tsaron kasar ta Tajiskitan.
Kafofin yada labarai na cikin gida sun bayyana cewa jirgin na iya zamowa mallakar kasar ta Tajikistan ne ko kuma Rasha. Jami'an kasashen biyu sun musanta cewa jiragen su sun kai farmaki a yankin.
Facebook Forum