A wani rahoto da aka fitar yau Litinin daga ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake Geneva, kwanitin binciken yace, ya kamata a tuhumi janar Min Aung Hlaing, wanda shine shugaban sojojin Myanmar, da wasu manyan jami'an soji masu mukamin janar su biyar da laifin kisan kare dangi, da laifin kuntatawa bil'adama da kuma aikata laiffuffukan yaki. Tawagar ta bukaci kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tura batun kotun hukumta manyan laifuka ta kasa da kasa, ko kuma su kirkiro da kwamitin binciken wucin gadi ko, kotun wucin gadi ta mussaman domin gudanar da bincike kan lamarin.
Tawagar binciken, da hukumar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta goyi baya, ta bada rahoton ne bayan tambayoyin da suka yi wa darurruwan mutane daga cikin 'yan gudun hijiran Rohinya 700,000 da aka tilastawa barin gidanjen su a yankin arewacin jihar Rakhine zuwa Bangladesh.
Shaidu sun bayanna irin yadda aka gasa masu akuba da ya hada da yi wa mata fyade, da kona kauyuka kurmus, da kisan gilla. Daga karshe dai rahoton ya nuna cewa abin da sojojin suka aikata ya wuce ainihin barazanar tsaro.
Facebook Forum