Wani Babban Jami'in Gwamnatin Gabon Ya Ajiye Mukaminsa

Masu zanga zanga a birnin Libreville na kasar Gabon

Ministan shari’ar Gabon Seraphin Moundounga, ya yi murabus akan takaddamar sake zaban shugaba Ali Bongo, inda ya zama babban jami’in gwamnatin na farko da ya fara ajiye mukaminsa tun bayan da aka kamalla zaben.

Hukumar zaben Gabon ta bada sanarwa a mako da ya gabata cewa Shugaba Bongo ne ya lashe zaben, inda ya doke dan takarar jami’iyar adawa Jean Ping da kimanin kuru’u dubu biyar, abinda ya janyo zanga zanga da tashe-tashen hankula a kan tituna da yayai sanadiyar mutuwar mutane a kalla shida.

Moundounga ya bayyanawa gidan radiyon Faransa na RFI a jiya Litinin cewa gwamnati bata sauraren damuwan al’umma akan kawo zaman lafiya wanda shine yayi sanadiyar ajiye aikinsa.

A jiya Litinin kuma, madugun ‘yan adawar, Jean Ping da ya ayyana kansa a matsayin shugaban Gabon ya yi kira da a yi gagarumin yajin aikin na gama gari , yana cewar sawa tattalin arzikin kasar tarnaki zai matsewa gwamnati lamba. Sai dai kuma mutane kadan ne suka zauna a gidajensu jiya Litinin, wasu bankuna da shagogi a babban birnin kasar Libreville sun sake budewa biyo bayan tashin hankalin da ya gabata. Wasu mazauna birnin sun ce basu ji kiran a yi yajin aikin ba.