Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Mahukuntan Yamai Sun Rusa Daruruwan Shaguna dake Babbar Kasuwar Birnin


Kasuwar Yamai inda mahukuntar Nijar suka rusa wasu shaguna da aka gina da kwanukan jinka
Kasuwar Yamai inda mahukuntar Nijar suka rusa wasu shaguna da aka gina da kwanukan jinka

Tun farko gwamnan jihar Yamai Hamidu Garba ya bada sanarwar rushe shagunan saboda magance hadarin ababen hawa a wuraren da suka hada da kewayen kasuwar, da makarantu da asibitoci.

Gwamnan jihar Yamai shi ya jagoranci aikin rushewar shagunan cikin tsakar dare.

To amma halin kashe wandon da shirin ya haddasa ya sa wasu kungiyoyi sun tashi da nufin jawa gwamnan birki.

Kungiyoyin suna nuna yatsa ga mahukuntan Yamai.Habila Rabiu shugaban wata kungiya yace gwmnan yana neman ya wulakanta mutanen ne ya kuma tozartasu. Yace gwamnan tafarkin dimokradiya ya samu mulki saboda haka yakamata ya yiwa jama'ar adalci. A cikin gaggawa gwamnan ya kamata ya kira mutanen ya zauna dasu domin a samu sulhu.

'Yan kasuwar da matakin ya shafa sun zargi gwamnan da sabawa ka'ida domin wai da izinin hukumomi suka mallaki wuraren kasuwancinsu.

Amma gwamna Hamidu Garba yace hukumomin da 'yan kasuwar basu da gaskiya saboda sun san wurin da aka basu ba wurin kasuwanci ba ne. Wurin ajiye motoci ne. Yace an basu na wucin gadi ne kuma ba saya suka yi ba balantana su yi gini na din din din. Dama an basu lokaci kuma lokacin ya cika su tashi.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG