Amincewar da shugaba Salva Kiir ya yi, na zuwa ne kwana guda bayan da kwamitin tsaron mai mambobi 15 ya kai ziyara Juba, babban birnin kasar, domin ya nuna matsin lamba ga manyan jami’an kasar, na su amince da shirin aikawa da dakarun.
Wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin gwamnatin hadaka ta wucin gadi ta Sudan ta Kudu da kuma kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, ta nuna cewa bangarorin biyu sun ce zaman lafiyar al’umar kasar shi ne abu mafi muhimmanci.
A dai watan Agustan da ya gabata ne, shugaba Kiir ya ki amincewa da tura karin dakarun.
Yanzu haka bangarorin gwamnatin Sudan ta Kudu da rundunar sojin da Majalisar Duniya ke marawa baya, sun amince cewa nan da karshen watan nan na Satumba, za a samar da wasu kwararan matakan da za kawar da duk wata matsala da za ta iya kawo cikas wajen baiwa rundunar sojin damar gudanar da aikinta.