Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Sun Horas da 'Yansandan Nijar Tare da Basu Tallafin Motoci


Jakadiyar Amurka a Nijar Eunice Redeck take shan hannu da shugaban 'yansandan da suka samu horo
Jakadiyar Amurka a Nijar Eunice Redeck take shan hannu da shugaban 'yansandan da suka samu horo

Amurka ta tallafawa Nijar da horas da 'yansanda 250 da sojojin Amurkan 50 suka aiwatar tare da basu tallafin motoci 50 da wasu kayan aiki domin su dakile barazanar Boko Haram a kasar

Kimanin 'yansanda dari biyu da hamsin ne suka samu horo a fannin yaki da ta'adanci daga sojojin Amurka su hamsin.

Bayan wannan horon da suka samu 'yansandan zasu daga zuwa yankin Diffa, yankin da ya sha fama da ta'adancin Boko Haram. 'Yansandan zasu yi aikin sintiri akan iyakokin kasashen da Nijar ke makwaftaka dasu.

'Yansandan da suka samu horo
'Yansandan da suka samu horo

Motoci kimanin guda hamsin da sauran kayan aiki Amurka ta baiwa 'yansandan a matsayin tallafa masu kamar yadda kakakin hukumar 'yansandan kasar Keften Adili Toro Mai Nasara ya sanar.

Ayarin motocin da Amurka ta bayar
Ayarin motocin da Amurka ta bayar

Yace horon da 'yansandan suka samu ba'a taba samun 'yansandan da suka samu irin horon ba. Sojojin Amurka sun horas dasu akan yadda zasu yi yaki da 'yan Boko Haram. Idan kuma nasu mutanen sun jikata an koya masu yadda zasu daukesu a je a yi masu magani.

Banda motocin da aka basu an taimakesu da kayan sadarwa irin na zamani domin tuntubar juna tare da sanar da na gaba abubuwan dake faruwa koina suke.

Wasu cikin motocin da Amurka ta baiwa Nijar
Wasu cikin motocin da Amurka ta baiwa Nijar

A sakamakon horon magatakardan ministan cikin gida na kasar ta Nijar Idris Adamu ya bayyana fatan cin nasara da yaki da 'yan ta'adan Boko Haram wanda kasar da makwaftanta suka kaddamar domin murkushe ta'adanci da 'yan ta'ada.

Jakadiyar Amurka a Nijar Eunice Redeck tace yaki da ta'adanci bashi da iyaka saboda haka yaki da bala'in ta'adanci yana yawaita horo ga 'yansanda.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG