An Kara Tayar da Bom a Nyanya

Harin bom a Nyanya, kilomita 16 daga tsakiyar birnin Abuja, Afrilu 14, 2014.

Rahotanni dake zuwa daga babban birnin Tarayya Abuja, na cewa an kara samun tashin bom a kusa tashar mota ta Nyanya, inda aka samu fashewar bom sama da makonni biyu da suka wuce.
Misalin bayan karfe 8 na yamma ne, wakilin Muryar Amurka, Saleh Shehu Ashaka wanda yake Otel din Transcorp yaji karar fashewar bom, duk da cewa akwai tazara mai tsawo tsakanin unguwar Nyanya da otel din.

Ashaka yayi kokarin zuwa inda abun ya faru, amma jami'an tsaron Najeriya sun toshe duk wata hanya dake zuwa unguwar. Sai dai yayi magana da wasu mazauna unguwar, wadanda suka shaida cewa bom din ya fashe a kusa da Masallacin Juma'ar Nyanya.

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-hikaya ya bada shaidar jin karar fashewar bom din, wadda ta saka jami'an tsaro dake tare dashi daukar matakan gaggawa a unguwar Area 1. Da Nasirun ya bincika, mazauna unguwar sun bada shaidar cewa an samu asarar rayuka kusan 20, sannan motoci na ci da wuta.

Jami'an asibitin Asokoro dake Abujan sun tabbatar wa Muryar Amurka da rashe-rashen rayuka da aka samu, inda aka kai gawarwarkin wadanda abun ya shafa.

Wani jami'in 'yan sanda, ya shaida cewa bom din, a mota aka hada shi.

Sama da makonni biyu kennan, tagwayen boma-bomai suka tashi, kuma suka kashe mutane kusan 70 da raunata sama da dari.

Jama'a yanzu na mamakin faruwar wannan abu, duk da cewa an tsaurara matakan tsaro a birnin na Abuja bayan fashewar bom din farko.

Your browser doesn’t support HTML5

Bom Ya Kara Fashewa a Nyanya - 5'01"