Shin wai hukuncin da aka yanke ma sojojin Najeriya 59 na kisa bisa samun su da akayi da take hakin bil’adam yayi dai dai kuwa? Farfesa Abdullahi Zuru na jami'ar Abuja, ya kira wannan hukunci da sunan bita da kulli.
Ya nuna cewar babu inda akace idan kana shugaba kuma kai ne me kara kuma kazama maiyanke hukunci. Don akwai tabbacin bazakayi ma wanda ake zargi adalci ba, bisa ga wannan dalilin da ma wasu, wanda idan akayi irin wannan shari’ar a boye to wadanda akayi ma wannan shari’ar na da hurumin su daukaka kara zuwa kotun farar hula, don neman hakinsu. Kuma anyi irin wadannan shari’oin a Gwantanamo wanda shugaban kasar Amurika Barak Obama yabada umurni abasu damar neman hakinsu na ‘yan adam.
Yayi bayani cewar ana sa ran wannan hukunci zai iya chanzawa tunda yanzu muna mulkin demokradiyya ne, don haka akwai tunanin za su daukaka kara wanda babu mamaki idan aka samesu basu aikata abun da ake tuhumarsu da shiba to za’a iya sakinsu.
Your browser doesn’t support HTML5