Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Wanke Sanata Ali Modu Sheriff Akan Boko Haram


Sanata Ali Modu Sheriff
Sanata Ali Modu Sheriff

‘Yan kungiyar Boko Haram, Sun dade suna musgunawa jama’ar, arewacin Najeriya.

‘Yan kungiyar Boko Haram, Sun dade suna musgunawa jama’ar, arewacin Najeriya, ta hanyar ta’addanci, inda har aka danganta Sanata Ali Modu Sheriff, da kungiyar.

Hukumar tsaron fari kaya ta Najeriya, DSS, ta wanke, sanata Ali Modu Sherrif, akan zargin da akeyi masa na cewa yana da hannu a Boko Haram.

Inda hukumar ta nuna wasu mutun bakwai, da tace sune suka kullawa Sanata Sheriff, sharri, ta hanyar mai sulhun nan na Australiya, Stephen Davis, mutun bakwai din dai sun hada da Junaidu Idris Khadi, da hukumar ta DSS, tace mai taimakawa Gwamna Kashim Shattima, na jihar Borno, ne wanda aka ce ya sami kimanin, Naira Miliyan hudu don lankayawa Sherrif, sharrin cewa shine maigidan ‘yan Boko Haram.

Sanata Sheriff, ya tara manema Labarai, inda yace gaskiya tayi halinta, yace kuma zai je kotu don neman diyyar bata masa suna.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG