Rundunar ‘Yan Sanda Najeriya ta musamman dake karkashin ofishin sifeta janar na ‘yan sanda ta sami nasarar damke wani jagoran masu garkuwa da mutane da kuma wadanda ke samar masu da bindigogi da harsasai.
Da yake bayani ga manema labarai a ofishin ‘yan sanda, daya daga cikin mutanen da suka shiga hannu ya bayyana cewa, rashin aikinyi ya sa ya shiga satar shanu kafin ya gamu da wani wanda ya nuna masa garkuwa da mutane yafi riba, wadda a fitar farko ya tashi da naira dubu hamsin akasin dubu goma zuwa sha biyar da yake samu ta hanyar satar shanu.
Banda masu garkuwa da jama’a domin neman fansa, rundunar ta kuma kama wadanda suke samar masu da makamai da kuma harsasai, da suka hada da wani dattijo dan shekara saba’in da tara, wanda ya bayyanawa Sashen Hausa cewa, shi tsohon maharbi ne, ya kuma shiga sana’ar saida bindigogi ne da yake samu daga hannun wani da yace yana samu a bakin ruwa inda ake sauke kaya.
Daga cikin wadanda aka kama akwai wani mutum da a ranar aka ce ya sayar da harsasai dubu daya ga masu satar mutane.
Su dai wadannan barayin suna aiwatar da wannan mummunar sanaar tasu ce akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Rundunar ‘yan sandar tace ba zatayi kasa a gwiwa ba har sai ta murkushe masu wannan mummunar sana'ar cikin kasa.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya aiko daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5