Wadanda suka sace shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Filato kuma tsohon ministan wasannin Nigeriya, sun sakoshi tare da mutane hudun da suka yi garkuwa dasu.
A karshen makon da ya shige ne, da yamma, aka sace shugaban tare da wani kusa a jam'iyyar Emmanuel Mannil da wasu mutane uku a yankin Jere cikin jihar Kaduna a kan hanyarsu ta zuwa Abuja wajen taron kasa na jam'iyyarsu da aka kammala jiya Lahadi.
Kakakin jam'iyyar a Filato Mr. John Akans ya tabbatar da sako shugaban da mutane hudun dake tare dashi. A cewarsa suna cikin koshin lafiya. Ya yiwa Allah godiya tare da wadanda suka taimaka aka sakosu.
Inji Mr. Akans Allah ne kadai ya kiyayesu domin jikin motar da suke ciki yayinda aka sacesu duk an yi mata raga-raga da harsashi. Ya ce yana gida yana hutawa daga azabar da suka sha.
Wadanda suka yi garkuwa dasu sun ce yunwar da gwamnatin yanzu ta jefasu ciki ta sa suke sace mutane. Wai ba sonsu ba ne. Injishi an tilasta wa shi Sango ya yi tafiyar awa 24. Da aka sakosu da dare an basu tocilan sun kuma yi tafiyar awa 22. Bugu da kari sun yi kwana uku babu ci ko sha.
Dangane da kudin fansa na kusan Nera miliyan dari da barayin suka nema a basu, Mr. Akans ya ce shi bashi da bayanin da zai bayar. Sai sun samu cikakken bayani tukunna.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum