Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Sace Yaro Ne Saboda Son Kudi – inji wasu miyagu


Wasu miyagun da aka kama su wanan baya
Wasu miyagun da aka kama su wanan baya

Bayan da dubun wasu miyagu ta cika ta yadda babu kuma sauran karya, sai su ka amsa cewa tsabar son abun duniya ne ya kai su ga sace yaro dan shekaru uku da haihuwa, wanda su ka bukaci iyayansa su biya miliyoyin kudin fansa matukar su na son dansu.

Miyagun nan da su ka sace wani yaro dan shekaru uku da haihuwa a kofar gidansu, sun fada ragar ‘yan sandan ciki kuma sun fito da yaron lafiya yau.

Da su ke bayanin musabbabin shiga wannan mugun aikin da su ka yi, masu sace mutanen, wadanda matasa ne da su ka hada da Umar Salisu dan shekaru 27 da Jamilu Alasan dan shekaru 30 da kuma Abba Tijjani mai shekaru 17 da haihuwa, sun amsa cewa tsabar son kudi ne ya ingiza su har su ka sace yaron mai suna Suleiman. Su ka ce dukkansu ‘yan unguwar Dawanau ne.

Malam Rabiu Garba shine ya jagoranci tawagar jami’an hukumar ta ‘yan sandan cikin na DSS wajen kama wadannan matasa da kuma ceto yaron da sukayi garkuwa dashi. Y ace bayan da su ka samu labarin abin da ya fari sais u ka tashi haikan wajen ganin sun kamo miyagun. Y ace lashakka miyagun za su gane kurensu. Ya kuma tabbatar da samun yaron cikin koshin lafiya.

Shi kuma mahaifin yaron, Alhaji Ibrahim Suleiman, y ace lokacin da aka gaya masa cewa an ceto dansa ya yi tsammanin mafarki ne yak e yi. Y ace sam bai ba jami’an tsaron ko kwabo ba. Yan a mai cike da godiya ga hukumar ‘yan sandan ciki ta DSS.

Ga dai wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:

Mun Sace Yaro Ne Saboda Son Kudi – inji wasu miyagu
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG