Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Yaro ya Mutu a Hannun Masu Garkuwa da Shi


Masu satar mutane
Masu satar mutane

Wani yaro dan shekaru takwas ya mutu a hannun masu garkuwa da shi a Kano gabanin su karbi kudin fansa naira miliyan biyu da suka nema daga iyayen sa.

A ranar Lahadi 31 ga watan Disambar shekara data gabata ne wani saurayi mai suna Abubakar dan shekaru 24 yace sun hada baki da matar sirikin sa Malama Wasila Abdullahi domin sace daya daga cikin ‘yayan kishiyar ta da nufin karbar kudin fansa daga mahaifin yaron Alhaji Ahmad Aliyu Umar mazaunin unguwar Kofar Ruwa dake a birnin Kano.

To amma a sai kawai masu garkuwar suka dauki dan ita wacce ta aike su na cikinta mai suna Usman maimakon dan kishiyarta marigayiya. Bayan ya shiga hannun jami’an tsaro na DSS, Abubakar yace da farko ya fada mata cewar ba zai iya yin wannan aikin ba, amma daga bisani ta bashi kudi domin ya samo wadanda zasu yi wannan aiki.

Sai dai ita Wasila Abdullahi ta musanta cewa ta bada kwangilar sace dan kishiyar ta ta. Shi ko mijin nata Alhaji Ahmad Aliyu ya yi wa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari karin haske game da tattaunawa da suka yi da masu garkuwar a kan batun kudin fansa naira miliyan 2 da suka nema inda ya nuna yadda lamarin ya jijjiga shi.

A nasa bangaren, Rabiu Garba dake zaman babban jami’in kula da harkokin bincke a hukumar DSS ta Kano yace binckiken da suka gudanar ya cimma nasara kuma suna ci gaba bin diddigin al'amarin.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:22 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG