Zaben ana yin shi ne tsakanin tsohon shugaban kasar Mahaman Ousman na jam’iyar RDR Canji ta ‘yan hamayya da tsohon ministan cikin gida Bazoum Mohamed na PNDS Tarayya mai mulki.
A yayin gudanar da yakin zabe kowanne daga cikin ‘yan takarar 2 ya yi ikaririn lashe zaben don maye gurbin Shugaba Issouhou Mahamadou wanda ke shirin kammala wa’adin mulkinsa na shekara biyar-biyar sau biyu.
Kimanin ‘yan Nijar 74,46000 da suka yi rajistar zabe ne ake saran za su fito a wunin ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu domin zaben wanda zai shugaganci kasar ta Nijar a tsawon shekara 5 masu zuwa.
Rumfunan zabe akalla 25,978 aka yi tanadi a dukkan fadin kasar wadanda kuma ke bude kofofinsu da karfe 8 na safe su rufe da karfe 7 na yamma agogon Nijar da Najeriya.
An dai gudanar yakin zabe cikin zazzafan yanayi abin da ke fayyace yadda bangarorin ke daukan wannan zabe da muhimmanc.
Bayan zagaya yankuna 8 na kasar ta Nijar, dan takarar jam’iyyar RDR Canji ta ‘yan hamayya Mahaman Ousman ya jaddada cewa ya a da kwarin gwiwar shi zai yi nasara a wannan fafatawa.
“Ni na yi imani, da yadda kuka yunkura a wancan karo (zagaye na farko) ba bu shakka, sa’a tana tare da mu bi’iznillahi.” In ji Ousman.
Ya kuma kara da cewa, “mu fuksanci wannan zabe cikin lami lafiya, kuma tare adalci da bai wa wanda ya ci hakkinsa, wanda bai ci ba kuma a ba shi hakuri.”
To sai dai dan takarar PNDS mai mulki bazoum ya yi ikirarin doke abokin karawarsa a wannan zabe a bisa la’akari da yadda yake samun goyon baya daga manyan jam’iyun siyasar da suka taka rawar gani a zagayen farko.
“Babbu shakka muna bisa hanyar nasara, za mu kasa su a ranar 21 ga wannan wata. A zauna lafiya, wanda kuma ya ce bai yadda ba, ya fito mu gan shi a ranar.” In ji Bazoum.
Bazoum ya kara da cewa, “za mu kasa su, ba bu sata, ba bu coge karkashin sa idon wadanda za su zo daga kasar waje domin su bi wannan zabe su kuma lura d ayadda aka gudanar da shi.”
Dubban jami’an sa ido daga ciki da wajen kasar ta Nijar ke Shirin zagaya sassan kasar don ganewa idannuwansu abubuwan da za su wakana a tsawon wunin na ranar Lahadi.
Hakan na faruwa ne yayin da hukumar ta kasa CENI ke cewa ta kammala shiri tsaf don ganin komai ya gudana cikin kyaukkyawan yanayi sannan ta gargadi ‘yan kasar ta Nijar su guji aikata abubuwan da za su janyo fitina bayan la’akkari da take-taken wasu daga cikin magoya bayan ‘yan takarar biyu.
Mahaman Ousman mai shekara 71 a duniya masani ne da ya karanci ilimin kididdiga ya kuma shugabanci kasar ta Nijar daga 1993 zuwa 1996 yayin da Bazoum Mohamed mai shekara 61 da haihuwa ya karanci ilimin falsafa kuma sau biyu yana rike mukamin ministan harakokin waje.
A baya-bayan nan ya rike mukamin minisatn cikin gida na tsawon shekara sama da uku kafin ya ajiye aiki da nufin tunkarar babban zabe Nijar na 2020 da 2021.
A zagayen farko na ranar 27 ga watan Disamba Bazoum Mohamed ya zo na 1 daga cikin ‘yan takara 30 da suka fafata inda ya sami kashI 39 da ‘yan doriya daga cikin 100 na kuri’un da aka kada sai Mahaman Ousman wanda ya zo na biyu da kashi 16 daga ‘yan kai. Dukkan ‘yan takarar biyu sun fito ne daga yankin Zinder.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5