USAID Za Ta Fara Horar Da Matasa 'Yan Shekaru 15 - 21 Wadanda Ba Sa Zuwa Makarantun Zamani a Kano

Taron USAID da kungiyar ta TEENSMATA a jihar Kano

A kokarinta na kula da rayuwar matasa, a fannin kiwon lafiya da ilimin zamantakewa da kuma dogaro da kai a tsakanin kasashe masu tasowa, hukumar raya kasashe ta Amurka-USAID ta dauki nauyin wani shirin bunkasa rayuwar matasa ‘yan shekaru 15 - 21, musamman wadanda ba sa zuwa makarantun boko.  

Shirin wanda wata kungiya mai lakabin TEENSMATA mai hadin gwiwa da gwamnatin jihar Kano ke aiwatarwa na samun kudaden tafiyar da shi daga hukumar ta USAID mallakar gwamnatin AMURKA dake tallafa wa kasashe masu TASOWA.

Madam Zainab Munkarim, ita ce daraktar da ke kula da aikace-aikacen kungiyar ta TEENSMATA a jihar Kano ta yi Karin bayani dangane da abin da su ke muradin cimmawa. ”Lafiyar matasa, musamman masu aure da marasa aure, ga wadanda ke da aure za a shigar da batun tazarar haihuwa da abubuwan da suka shafi al’adar mata ta wata-wata kana da sha’anin cin zarafin jinsi da shugabanci”.

Yanzu dai kusan shekaru biyu kenan da suka shude, shirin ya bude zaurukan bada shawarwari da tarbiyyantar da matasan a kanan hukumomin Wudil da Ungogo a nan jihar Kano a matsayin tsarin gwaji kuma ga alama kwaliyya ta kama tafarkin biyan kudin sabulu. “Na taso a gidanmu na ga ba a kai ‘yaya mata makarantun zamani, sai dai na addini, amma maza suna karatun boko, saidai zuwa na wannan cibiya na koyi abububuwa da dama da suka shafi zamantakewa kaina ya waye na san ‘yanci na, in ji wata matashiya mai suna Ruqayya Abdulwahab.”

Taron USAID da kungiyar ta TEENSMATA a jihar Kano

Baya ga gwamnatin jihar Kano da hukumomin, Shirin na TEENSMATA na aiki kafada da kafada da hukumomin gwamnatin tarayya da-ma cibiyoyi masu zaman kansu masu alaka da tsarin aikace aikacen da suke aiwatarwa.

Cibiyar horas da matasa Sana’oi ta Sani Abacha na cikinsu, kuma Comrade Yahya Shu’aibu Ungogo da ke zaman daraktan hulda da Jam’a na cibiyar ya fayyace rawar da zasu taka domin cimma nasara.

“Yanda za muyi kokari mu hada kai da gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha domin Shirin ya dore bayan hukumar USAID ta kammala wa’adin da ta shata wa Shirin.”

Babban buri da fatan hukumar USAID ta gwamnatin Amurka shi ne gwamnatocin Najeriya a matakai daban daban su rungumi wadanann manufofi da tsare tsare domin ci gaba mai dorewa.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

USAID Za Ta Fara Horar Da Matasa Shekaru 15 - 21 Wadanda Ba Sa Zuwa Makarantun Zamani a Kano