Jagoran tawagar 'yan majalisun ya bayyana dalilin ziyarar tasu yayin da yake jawabi a ofishin jakadancin Amurka dake Abuja.
Jagoran yace sun zo su ji abun da suke son ji daga gwamnatin Najeriya. Batutuwan da suka biyo sawunsu sun hada da hakin bil Adama da ceto 'yan matan Chibok da kuma kawo karshen ta'adancin 'yan Boko Haram.
'Yan majalisun sun nuna damuwarsu da batun cin hanci da rashawa da suka yiwa kasar katutu. Wadannan abubuwa sun mamaye rayuwar 'yan Najeriya lamarin da ka iya yin tarnaki da kokarin yaki da ta'adanci.
Shugaban tawagar ya roki 'yan Najeriya da su hada kai da gwamnatin Shugaba Buhari domin a tabbatar an murkushe ta'adancin 'yan Boko Haram
Shugaban tawagar yace Amurka bata damu da inda shugaban Najeriya ya fito ba. Abun da suke so shi ne a samu kyakyawan shugabanci. Yace ya san shugaba Buhari a matsayinsa na tsohon janar din sojojin Najeriya saboda haka ko shakka babu maganar Boko Haram zata zama tarihi kwanan nan.
Ita ma wata 'yar majalisar dokokin Amurka tace saboda irin barnar da 'yan Boko Haram ke yiwa jama'a akwai bukatar 'yan Najeriya su hada kai da gwamnatin yanzu domin a samu mafita.
'Ya'yan kungiyar nan dake fafutikar a sako 'yan matan Chibok da aka sani da Bring Back Our Girls sun mamaye ofishin jakadancin Amuraka a Abuja kana suka gana da 'yan majalisun na Amurka.
Hadiza Bala Usman da ta jagoranci kungiyar ta yiwa Muryar Amurka karin bayani.Tace yanzu sun samu tabbas cewa gwamnati zata yaki Boko Haram gadan gadan. A wannan shekarar za'a kawo karshen Boko Haram. Za'a kuma ceto 'yan matan.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5