Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Zata Binciki Ma'aikatanta Wadanda Suka Arzurta


'Yan Najeriya suke zanga-zanga kan cire tallafin mai, suna zargin cin hanci d a rashawa.
'Yan Najeriya suke zanga-zanga kan cire tallafin mai, suna zargin cin hanci d a rashawa.

Hukumar hana zarmiya ICPC ta haskaka fitila kan ma'aikata wadanda rayuwars a ta tadara labashinsu.

Ma'aikata wadanda suke amfani da mukamansu wajen arzurta kawunansu zasu fuskanci ICPC, a wani sabon yunkuri tsarkakewa da kuma tsabtace ma'aikatan gwamnati.

Hukumar hana zarmiya da dukiyar jama'a ICPC, tace zata binciki ma'aikatan gwamnati wadnada suka arzurta, kuma babu yadda za'a yi ace albashinsu ne sarsalar dukiyarsu.

Hukumar zata duba ajiyarsu a bankuna,kadarori da suka mallaka kamar gidaje mallaka a Legas da Abuja, da wasu sassan Najeriya.

Wasu ma'aikatan gwamnati da suka bayyana ra'ayoyinsu kan wannan shiri, sun bayyana goyon bayansu, suna cewa ai irin wadannan mutane suna suka arzurta kansu ba Allah ne ya arzurta su ba. Sabo da irin son zuciyarsu ayyukan da suka kamata a yi domin moriyar talakwa hakan bai samu ba.

Wasu kuma suka ce wannan mataki zai zama ishara ga ma'aikata masu tasowa su san cewa doka ba zata bar su idan ta riske su daga irin take-takensu.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG