Cikin ayyukan kwamitin tallafawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, karkashin jagorancin tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya, harda sake tsugunar da mutane da hare haren suka shafa, da inganta rayuwarsu.
Mazauna wasu sassan jihohin arewa maso gabas, yankin da hare haren 'yan binidgar tafi shafa, suna bayyana ra'yiyinsu kan umarnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar, na a baiwa kwamitin TY Danjuma Naira Bilyan biyar.
Da dama cikin mutanen suka ce matakin sara ne kan gaba. Saura kawai shugaban kasa ya kara sa ido domin ganin kudaden an yi amfani da su kan hanyar da aka bada su.
Wani mutum da yayi magana da wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, yace idan aka ziyarci wasu sassan jihar Adamawa kamar Mubi,da Michika, da Lassa, da kuma a jihohin Borno da Yobe, babu alamun mazauna yankin sun sami ko wani irin taimako.
Yace wuraren basu da hanyoyi, babu asibitoci, gadoji da hanyoyi sun lalace, babu noma, kai hatta iri, yace yanzu ya gagari mutane.
Alhaji Ibrahim Mohammed 86, wanda shine mataimakin shugaban kungiyar 'yan kasuwa ta kasa na shiyyar jihohin arewa maso gabas, yace babu dan kasuwa da ya sami taimako ko wani iri daga gwamnati. Yace 'yan kungiyar a wannan yanki, jarinsu ya karye, sabo da haka suna neman taimako domin sake fafadowa.
Ga karin bayani.