Uku Daga Cikin ‘Yan bindigar Da Suka Sace Daliban Bethel Sun Shiga Hannu

Mutanen da ake zargi da hannu a satar daliban Bethel (Shafin yanar gizo/Channels TV)

A farkon watan Yulin bana ‘yan fashin daji suka shiga makarantar ta Bethel suka yi awon gaba da dalibai maza da mata sama da 100.

Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar ‘yan sandan kasar ta sanar da kama uku daga cikin ‘yan bindigar da suka sace daliban makarantar Bethel Baptist a Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Kakakin hedkwatar 'yan sanda Frank Mba ya ce an kama Adamu Bello, Isiaka Lawal da Mu’azu Abubakar wadanda suka amsa cewa suna da hannu a satar daliban.

A farkon watan Yulin bana ‘yan fashin daji suka shiga makarantar ta Bethel suka yi awon gaba da dalibai mata da maza sama da 100.

‘Yan sandan na Najeriya sun gabatar da mutanen ga Manama labarai da ake zargin sanye da kakin soja.

Binciken farko ya nuna cewa, wadanda ake zargin sun ce su 25 suka jagoranci satar daliban suna masu cewa sun kitsa harin ne don neman kudi.

Yayin da yake jawabi a lokacin gabatar da ‘yan bindigar, Mba ya ce cafke mutanen na daga cikin nasarorin da rundunar ‘yan sandan ta musamman ta samu.

Ya kara da cewa, ana nan ana ci gaba da bincike a kokarin da ake yi na gano sauran wadanda ke da hannu a harin.

An dai sako daliban da dama a lokuta daban-daban inda ko a ranar Asabar da ta gabata aka sako wasu karin mutum 10.

Bayanai sun yi nuni da cewa yanzu akwai akalla dalibai 20 da suka rage har yanzu a hannun ‘yan bindigar.