KADUNA, NAJERIYA - Sai dai har zuwa yammacin yau Litinin babu labarin wadanda aka shiga daji da su.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, da ya tabattar da sace mutanen 87, ya kara da cewa tuni jami'an ‘yan sanda su ka bi sahun 'yan-bindigan har cikin daji don kubutar da wadan da aka sace.
Mataimakin Shugaban karamar hukumar Kajuru, Hon. Daniel Ayuba dan asalin garin Kajuru station din da 'yan-bindigan su ka afkawa ne kuma ya ce dama suna fama da matsalar tsaro domin cikin wadan da aka sace har da wadda kwanan ta daya da dawowa daga hannun 'yan-bindigan kuma an sake sace ta.
A wani abu mai kama da sabon salo dai 'yan-bindigan sun shiga garin Kajuru Station ne ba tare da harbin da zai sa a ji shigar su garin ba, inda su ka dinga fasa gidaje su na dibar mutane, mata da maza har da yara, kamar dai yadda daya daga cikin wadanda aka sace musu iyali ya shedawa Muryar Amurka.
A jere dai cikin makonni biyu, 'yan-bindiga sun shiga garuruwa uku kenan a karamar hukumar Kajuru inda su ka sace mutane sama da mutane 140 banda dalibai 287 da 'yan-bindigan su ka sace a karamar hukumar Chukun din dake makwabtaka da Kajurun duka a shiyyar tsakiyar Kaduna.
A saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5