Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Musanta Kai Harin Ramuwar Gayya Bayan Kashe Sojoji 16


Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)
Sojojin Najeriya (Facebook/Rundunar sojin Najeriya)

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya musanta zargin da ake yi wa rundunar sojojin kasar na hannu a kone-konen gidaje a wani kauyen jihar Delta inda wasu matasa suka kashe dakarunta da aka aika aikin wanzar da zaman lafiya.

WASHINGTON, D. C. - Mazauna yankin sun ce sojoji sun kai hari a unguwar Okuoma da ke gefen kogin mai mutane dari ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da suke neman wadanda ke da alhakin kashe-kashen na ranar Alhamis

Janar Christopher Musa
Janar Christopher Musa

Tam Oburumu, wanda ya gudu daga gidansa, ya ce wasu mutane sanye da kayan yaki suna yawo suna tona wurare suna neman makamai a gidaje kafin su kona su, inda yace “barnar da aka yi a yanzu tana da yawa, an kona gidaje da dama”.

Oburumu ya ba da shaidar haka ta wayar tarho daga wani kauye da ke kusa bayan ya nemi mafaka. Kaddarori mallakar gwamnati, ciki har da makarantar firamare da asibiti ne kawai suka tsira, in ji mazauna.

Shugaba Bola Tinubu ya ce ya bai wa sojoji cikakken ikon farautar wadanda ke da alhakin kashe sojojin, wanda ya bayyana a matsayin "laifi na rashin tausayi ga al'ummar Najeriya."

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Sai dai babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ya musanta cewa sojoji sun kai wa al'ummar yankin hari.

"Babu wani ramuwar gayya daga sojojin, muna neman wadanda suka yi kisan gilla da ma'ajiyar makamansu," in ji Musa a wani sako da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ana dai yawan samun tashe-tashen hankula, wani lokacin kuma ana samun asarar rayuka, kan filaye ko kuma biyan diyya kan malalar man da kamfanonin makamashi ke yi a yawancin al'ummomin na jihar Delta.

Amma wata ‘yar kasuwa mai suna Friday Addy a Okuoma ta ce ita da mahaifiyarta sun fice daga gidansu lokacin da sojoji suka isa.

Mutane sun gudu don tsira da rayukansu, kuma da yawa sun bace kuma ba za mu iya gano su ba. Ba mu da wani taimako," in ji Addy.

Gabanin afkuwar lamarin a ranar Alhamis 14 ga watan Maris din da muke ciki, rahotanni na cewar, sojojin da aka yiwa kisan gillar sun amsa wani kiran gaggawa ne sakamakon wata hatsaniya tsakanin al'umomin Ukuoma dana Okoluba.

Da yake tabbatar da afkuwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Asabar, mai Rikon Mukamin Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaro, Burgediya Janar Tukur Gusau yace wasu matasa ne suka yiwa sojojin da aka kashe din kofar rago sa'ilin da dakarun Bataliyar Sojan Ruwan Najeriya ta 181 ke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a karamar hukumar Bomadi ta jihar Delta.

A cewar sanarwar, mummunan al'amarin ya faru ne sa'ilin da dakarun suka kai dauki game da wani kiran gaggawa sakamakon barkewar rikicin kabilanci tsakanin al'umomin Ukuoma dana Okoluba dukkaninsu a jihar Delta.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG