Twitter Ya Bayyana Riba Duk Da Matsalar Da Yake Fuskanta

Kamfanin sada zumunta na Twitter, ya bayyana ribar karin kudaden shiga da ya samu a karshen shekarar da ta gabata, kuma hannayen jarin kamfanin ya karu tun kamin bude kasuwar hada-hadar kasuwanci a jiya.

Duk dai da cewar sakamakon ya ja hankalin kasuwar hannayen jari na Wall Street, amma hakan bai magance matsalar da kamfanin ke fuskanta ba. Kamfanin na fama da matsalar zage-zage, asusun karya, kana da matsalar kutse na gwamnatin kasar Rasha.

Kamfanin na cigaba da fuskantar matsalar karuwan abokan hurda, wanda mutane da dama basa amfani da kafar wajen mu’amalolinsu na yau da kullun.

Duk a cikin wannan yanayin shugaban kamfanin yayi murabus, yanzu haka kamfanin na fuskantar matsalar shugabanci, wanda hakan yasa kamfanin fito da wasu dabaru don magance matsalar labarai marasa tushe.