Babban jami’in kula da makaurata na Kungiyar Tarayyar Turai yace mai yiwuwa ne Brussels ta hana bada tallafin inganta rayuwa ta kuma kafa dokar da zata shafi huldar cinikayya da kuma takaita bada takardar izinin shiga yankin kan kasashen Afrika da kuma Asiya yankunan makauratan na asali, da nufin tilasawa kasashen karbar mutanen da aka hana mafaka a kasashen turai.
A hirarsa da jaridar kasar wallafa yau asabar, Dimitris Acramopoulos yace, jami’an KTT suna duba yiwuwar dakatar da daukar nauyin manyan ayyukan bunkasa kasashen. Yace, muna kashe kudi ne a wadannan kasashen da nufin samar da dama ga al’umma.
Yace kasashen da suka gaza bada hadin kai zasu iya fuskantar hanasu takardun izinin shiga turai baki daya. Jamus tayi barazanar hana kasashen da suka ki karbar masu komawa gida, takardun izinin shiga kasar.
Sai dai bisa ga dukan alamu Acramopoulos yana nuna za a fadada hana takardun izinin shiga kasashen da zai shafi dubban ‘yan kasashen ketare kama daga jami’an diplomasiya, da likitoci, da dalibai, da masu gudanar da bincike.