Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Jamus Ta Kai Ziyara Nijar Domin Tattaunawa Kan Harkokin Tsaro


Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da Shugabar Jamus Angela Merkel
Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da Shugabar Jamus Angela Merkel

Mahimmancin kasar Nijar a yankin Sahel bisa harkokin tsaro ya sa Majalisar Dokokin kasar Jamus kai ziyarar tattunawa da 'yan majalisar Nijar din

Kasar Nijar na yankin da masana harkokin tsaro suka bayyana na da mahimmanci wajen daukan matakan karya lagon kungiyoyin ta'addancin da suke cikin kasashen yankin Sahel.

Mahimmancin ya ba da hujjar kafa sansanonin dakarun kasashen yammacin Turai a Nijar da makwafciyarta Mali. Shi ne kuma mafarin da ya sa Majalisar Dokokin Jamus ta aika da tawaga Nijar domin tattaunawa akan harkokin tsaro.

Onarebul Hamma Asan shugaban kwamitin majalisar dokokin Nijar dake kula da harkokin tsaro yace ba Nijar ko kasashen Sahel ne kawai ba ke fama da tsaro da ayyukan ta'addanci. Yana mai cewa harkokin tsaro sun shafi duka al'ummar duniya. Kowa na jin abubuwan dake faruwa a kasashen Spain, Faransa da duk kasar da 'yan ta'adda suka kunno kai.

Onarebul Hamma yace yanzu lokaci ya yi da duk kasashe, kama daga Afirka zuwa Turai, zasu hada kawunansu su yaki wannan bala'i tare domin a fita daga ta'addanci.

Samun labarai akan halin da sojojin Jamus ke ciki a bakin daga na cikin dalilan da tawagar ta Jamus ke ziyartar Nijar, musamman majalisa. Akwai sojojin Jamus da kayan aiki irin na zamani suna aiki kafada da kafada da sojojin Nijar a Agadez. Burin kasashen biyu dangane da kokarin murkushe ta'addanci ya zo daya.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG