Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daga Watan Fabrairun 2015 Zuwa Yau Boko Haram Ta Hallaka Mutane 540 a Nijar


Horas dAa hukumomin tsaron Nijar domin yakar Boko Haram
Horas dAa hukumomin tsaron Nijar domin yakar Boko Haram

Alkalumma sun nuna cewa kungiyar Boko Haram ta rutsa da mutane fiye da 540 a yankin Diffa, Jamhuriyar Nijar tun daga shekarar 2015 kawo yanzu da suka hada da mata da yara baicin wadanda suka yi batan dabo.

Rahoton hukumar dake kula da ayyukan agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa cikin mutane 540 da suka rasa rayukansu, ko suka jikata ,ko kuma aka yi awan gaba dasu sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ta kai jihar Diffa daga watan Fabrairun 2015 zuwa watan Agustan 2017, a garin Bosso ne lamarin ya fi kamari.

Garin na Bosso ya rasa mutane 230 kana 44 suka jikata. Uku kuma sun yi batan dabo. Sannan kuma aka yi awan gaba da uku. Birnin Diffa ya rasa mutane 73, sannan 96 suka jikata. An yi awan gaba da biyu. Wani garin ya rasa mutane 31 sannan hudu suka jikata aka kuma yi awan gaba da 47. A garin Mainasaro kuma mutane uku suka jikata, aka kuma yi awan gaba da biyu. A garin Gudun Mariya an yi awan gaba da mutane biyu.

Yayinda yake tsokaci kan rahoton Alhaji Salisu Ahmadu wani mai fafutika cikin kungiyoyin fararen hulan Nijar ya bayyana cewa lokaci ya yi da kungiyar Boko Haram za ta zama tarihi.

Yana mai cewa ya kamata kasarsu ta Nijar da sauran kasashen dake fafatawa da kungiyar Boko Haram su mayar da kungiyar yunwar cikinsu da zasu nema tukuru su kawar. Yace duk abun da aka sani kamar tattalin arziki ya ta'azara. Tattalin rayuwa babu shi. Babu makaranta, ba'a iya noma ko kiwo saboda muggan ayyukan kungiyar.

Ya kira asa kudi a ayyukan tsaro yadda ya kamata. Al'umma su ba da rahoton duk abun da basu yadda dashi ba. A dinga lura da abubuwan dake faruwa, da masu shigowa suna fita, a daina sakaci.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG