Tura ta Kai Bango a Wasannin Kwallon Kafa na Kasa da Kasa, Hukumar FIFA ta Fidda Jadawalin Yadda Za'a Gudanar da Wasan

National Stadium, 2014 World Cup, Brasilia, Brazil

An shirya gudanar da gasar wasannin kwallon kafa ne da la'asar a kasashen dake da yanayin zafi.
Hukumar kula da shirya wasannin Tamaula a kasa da kasa da a takaice ake kira FIFA, tace za'a ci gaba da shirya gudanar da wasan kwallon kafa na kasa da kasa domin cin kofin duniya a lokutan la'asar, duk da cece-kucen da hakan ke janyowa kamar yadda aka ji daga bakin shugaban hukumar Mr. Sepp Blatter, a wani jawabin bude taron jami'an hukumar wassanin kwallon kafa da aka gudanar ran Talata.Bayan wata fafatawar da aka yi wadda ta janyo maimaita yin wasan a ranar Juma'a.

Jawabin na babban Magatakardar hukumar ta FIFA Jerome Valcke, ya yanyo cece-kuce a tsakanin masu saurarensa lokacin da yayi kokarin yin karin haske kan yadda za'a yi aiki da tsarin maimaita yin wasan bayan anyi kunnen doki domin a fidda gwani, wanda kuma ta haka ne za'a iya gano gwanaye takwas daga cikin masu gasar a zagayen farko a wasannin motsa jikin da za'a gudanar shekara mai zuwa.

Yace ba abune mai sauki ba a fahimci abinda hakan ke nufi a karon farko, lallai kam yace ya yarda da hassashen da aka yi amma duk da haka yace kun gani saida ya dauki dogon lokaci domin tabbatar da cewar ya fahimci abinda ake nufi.