Wannan nasara da ta zo ta kafar dan wasan Najeriya mai suna Emmanuel Emenike, tana nufin cewa Najeriya ta dauki babban mataki na zuwa gasar cin kofin duniya shekara mai zuwa a kasar Brazil.
Emenike, ya jefa kwallon na biyu cikin minti na 90 a dalilin bugun fenariti da alkalin wasa ya bayar saboida wani dan wasan Ethiopia ya kayar da dan wasan Najeriya a kofar ragar 'yan Ethiopiar.
Za a kara zagaye na biyu ranar 16 ga watan Nuwamba a birnin Calabar dake kudancin Najeriya.
Kafin wannan bugun fenariti, Emenike ya jefa kwallon Najeriya na farko a minti na 67 da fara wasan, ya rama wa kasarsa ci dayan da aka yi mata tun kafin nan.
A dalilin wannan nasara da ta samu, yanzu kusan duk masu fashin bakin kwallo sun fara hasashen cewa Najeriya ce zata haye zuwa Brazil, abinda zai kawo karshen watanni 18 da 'yan wasan kasar Ethiopia suka yi su na bayar da mamaki a wasannin da aka yi na share fagen zuwa gasar cin kofin duniyar.
A sauran wasannin na yau da aka yi a Afirka, Burkina Faso ta doke Aljeriya da ci 3 da 2; Ivory Coast kuma ta doke Senegal da ci 3 da 1, duk a jiya asabar.
A yanzu haka da ake rubuta wannan labarin, Kamaru da Tunisiya su na gwabzawa, sun tafi hutun rabin lokaci, amma babu wadda ta jefa kwallo a raga har yanzu.